ABNA24 : Tashar Russia Today ta bayar da rahoton cewa, a wata zantawa da Ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergey Lavrov, ya jaddada cewa, babu wata tababa a kan martanin Rasha, a kan duk wani mataki na tsokana daga bangaren Amurka.
Ya ci gaba da cewa, a kowane lokaci Rasha tana fifita daukar matakai na diflomasiyya wajen warware batutuwa da dama da suka shafi siyasar kasa da kasa, maimakon nuna karfi ko tayar da jijiyoyin wuya, amma kuma hakan a cewarsa, ba yana nufin cewa Rasha za ta zura ido a kan duk wani mataki na tsokana a kanta ba.
Dangane da bukatar da shugaban kasar Joe Biden ya gabatar wa kasar ta Rasha, ta neman a shiraya wata ganawa ta musamman tsakaninsa da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin, ministan harkokin wajen kasar ta Rasha ya bayyana cewa, ba su da wata matsala kan hakan, kuma yanzu haka shi da kansa ne yake bin kadun wannan batu.
Dangantaka tsakanin Amurka da Rasha ta kara yin tsami tun bayan da Joe Biden ya karbi shugabancin Amurka, inda yake kallon Rasha a matsayin kasa da take babbar barazana ga Amurka, musamman ma zargin da ‘yan jam’iyyar Democrat masu mulki suke yi, a kan cewa Rasha ta yi kutse a cikin harkokin zaben kasar ta Amurka.
342/